
Zaharadeen Mziag, Muhammad Ali Hafizi @ Katsina City News
9/5/2023
A ranar Talata 9 ga watan Mayu kwana Ashirin kafin ƙarewar Gwamnatinsa, Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari da Mataimakinsa Qs. Mannir Yakubu yakai ziyarar Aiki gami da buɗe Makarantar Kiwon Lafiya ta GIAL COLLEGE OF HEALTH TECHNOLOGY AND ENVIRONMENTAL SCIENCE, dake Unguwar Kukar Gesa da akafi sani da Lambun Danlawan.
Makarantar da ta ƙumshi bangarorin Kiwon Lafiya, Aikin gona, Horas da Sana’o,i, sashin Ilimin kimiyyar zamani na na’ura mai ƙwaƙwalwa, da Babbar Asibitin Jinya da Unguwar zoma, wadda tsohon Danmajalisar Wakilai ta Tarayya daga Mazabar Katsina ya samar.
A lokacin da yake gabatar da makarantar da Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari Danlawan ya bayyana cewa wannan wani ƙuduri ne da ya daɗe da samarya na fiye da shekaru Talatin kuma har inda ake yau bai gaza ba kuma da yardar Allah duk wani abu, ko wani bangare da aka samar zai tabbata kwanannan saboda lokacin ne yazo. Hamisu gambo ya bayyana yanda makarantar ta GIAL COLLEGE OF HEALTH ta ke gudanar da Aikinta, da kuma ire-iren gine-ginen da ta samar da zasu dauki fiye da Ɗalibai dubu da masaukinsu na kwana da Azuzuwa, Ɗakin Karatu da wajen Gwaje-gwaje. Hon. Hamisu Gambo ya yaba wa ‘Yan majalisar jiha da Muƙarraban Gwamnati na yanda suka dauki nauyin karatun wasu dalilai da cikakkiyar Kulawa, a karshe yayi godiya ga Gwamnatin jihar Katsina ganin yanda ta bawa Ilimi Muhimmanci, yace wannan dalilin ma ne ya sanya muka samar da wani waje da zai dunga bada Horon sana’o,i ga Matasa da zamu cika da kayan Aiki wanda muka sanyawa sunan Maigirma Gwamna. Inji Danlawan.
Da yake maida jawabi Maigirma Gwamnan jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya yaba da kokarin Hon. Hamisu Gambo, inda yace yaci moriyar Rayuwar sa, saboda bada Ilimi yafi duk wani Aiki da zakai, yace balle ma shi wannan anginashi ne ba don a maida kudi ba, yace akwai hanyoyi da zasu kawo kudi fiye da wannan. Yace ” Idan ka gina Ilimi zaka iya sheru aru-aru ko bayan babu kai ana tunawa da kai, don haka muna tayaka murna.”
Gwamna Masari ya yi kira ga al’umma da su cigaba da yiwa shugabanni Addu’a domin dorewar mulki na gari, idan shugaba ya lalace to al’umma ce ta lalace, saboda duk wata Lalata akan al’umma zai sauketa. Masari ya bayyana cewa saura kwana ashirin dashi da abokin aikinsa Mannir Yakubu subar Mulki, yana kira da musamman ‘yan jihar Katsina da su goyawa Sabuwar Gwamnatin da zatazo baya kuma su tayata da addu’a.
Gwamnan Katsina ya samu rakiyar Mataimakansa, Irinsu Mataimakin Gwamna Qs. Mannir Yakubu, S.S.A Mai Turaka, Alh. Bature Masari, Dan majalisar wakilai na jihar Katsina Hon. Ali Abu Albaba da sauransu.