AN CIRE SARKIN DAJIN ZAZZAU DAGA HAKIMCI
DAGA MASARAUTAN ZAZZAU:-
MAJALISAN Masarautan Zazzau a zaman ta na musamman da safiyan yau bisa jagorancin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ta bayar da sanarwan ba tare da bata lokaci ba, na Cire Alhaji SHEHU UMAR, Sarkin Dajin Zazzau daga Hakimcin Gunduman Kubau na Karamar Hukuman Kubau a Jihar Kaduna.
Cire Alhaji Shehu Umar daga Hakimcin ya biyo bayan nuna rashin Da’a da sabama Dokoki da Ka’idojin tafiyar da aiki wanda ya jawo Barkewa da Tarzoma a cikin al’umman garin Pambeguwa.
A halin yanzun, Majalisan Masarautan Zazzau ta dauki mataki wajen gyarawa gami da daidaita al’amura a wannan yankin na Pambeguwa.
Signed:- ABDULLAHI ALIYU KWARBAI,
Media and Publicity Officer, Zazzau Emirate