Majalisan Masarautan Zazzau karkashin Jagoranci Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli, CFR ta bayar da umurnin Koran Malam SAMA’ILA ABUBAKAR RIMIN TSIWA Daya daga cikin Dogaran Fadan Zazzau daga aiki a Masarautan Zazzau.
Wata matashiya wanda take shirin Aure tazo Fadan Zazzau domin a sadata da Mai Martaba Sarkin Zazzau bisa neman taimako kan batun auren nata, ta gabatar da bayanan ta ga Malam Sama’ila wanda maimakon gabatar da ita zuwa inda ya kamata, sai ya yaudareta zuwa wani wuri dabam inda shi da Abokansa suka yi LALATA DA ITA.
Majalisan Masarautan Zazzau, ta umurci Rundunan ‘Yan Sanda da ta gaggauta kamalla bincike, kuma su gabatar da masu laifi cikin gaggawa a gaban Kotu domin yanke masu hukuncin dai-dai da laifinsu.
Haka kuma, Majalisan Masarautan Zazzaun ta dauki alkawarin bin sahun wannan batu domin tabbatar da an kwatanma wannan Matashiya hakkinta.