Gwagware Foundation.
Injiniya Muttaƙa Rabe Darma Muna baka shawara, idan zakayi magana kasan mi zaka fada. Maganar da kayi cewa;
“Dakta Dikko Umar Raɗɗa saida ya kashe kuɗaɗe dayawa sannan ya samu Takara”
Kai yanzu har kana da bakin magana wajen Lalata Siyasar jihar Katsina ta zama ta Kuɗi?
Ka manta a 2011 a lokacin zaɓen Tazarce na Jonathan, a lokacin kana riƙe da Kujerar PTDF? Ka manta taron da kayi gidan mariganyi Shehu Musa ‘Yar’adua, lokacin da kasa kaya irin na Jonathan, harda irin Sarkar da Jonathan ke sawa a wuya kasa?
Biliyan nawa kazo ka raba a gidan Shehu Musa ‘Yar’adua dake GRA domin Jonathan yayi Tazarce? A lokacin kama ƙi sanya kaya irin naka na Musulmi domin ka burge Jonathan, fadanci iri-iri da ɗan’iyanci ya maidaka Kujerarka, kai duk ka manta wannan yawan kuɗin da kazo ka kashe don Jonathan yayi Tazarce ya maidaka Kujerarka?
Bayan ka gama kashe kudin yaƙi maida ka Kujerarka, shine kai yanzu kaike da bakin magana cewa; wani ya kashe kudi a wajen Zaɓe? Zancen dama karya ne, bashi da tushe bare makama.
Kuma kai Injiniya Muttaƙa Munaso ka amsa mana wannan tambayar, mundai san yanda ka taho Katsina a 1999 Malamin Makaranta ne kai a BUK lokacin munsan Motar hawa ma, mun san yanda akayi kazo bayan angama Zaɓe, Ummaru Musa ya baka Kwamishina, a jihar Katsina. Sannan ya tafi Shugaban Ƙasa ya baka Shugaban PTDF to ina kasamu kudin da kasayi gidaje a Kaduna da Abuja, yanzu kake saidawa kana Siyasa da kudin.
To muna so kasan cewa wutsiyar Raƙumi tayi nisa da ƙasa, Dikko Radda ba tsaranka bane, baka ganin ko a takara kai ta mataimaki kake nema.
Wannan martani ga maganganun Muttaka Rabe da yayi da wata kafar watsa labarai.
Wannan shine kashin farko.
A saurare ni a kashi na biyu.
Injiniya muttaqa Rabe yayi wasu kalamai ne, akan Dan takarar mu na gwamnan katsina a inuwar APC Dr Umar Radda gwagwaren katsina. A wata kafar yada labarai na yanar gizo.