
@Katsina City News
Alhaji Ibrahim Bindawa Sarkin Labarai na Mai Martaba Sarkin Katsina, ya Mayar da Martani akan wani labari da Jaridun Katsina City News suka buga a yau 20/9/2022
Labarin mai taken: GINI MAI TSOHON TARIHI A GIDAN SARKIN KATSINA YA RUGUJE.
Sarkin labarai ya yiwa babban Editan Jaridun bayani, akan labarin yace, Sam, a gidan babu wani gini da ya ruguje.
Yace; Akwai gyara da ake yi, na kara ingatanta wadannan dakunan da ake magana, kuma an Dade ana aikin.
Wanda Mai Martaba ya amince, ayi kuma yanzu ake aikin sosai kafin dawowarsu.
Sarkin labarai, ya kara da cewa a wajen aikin ne, wani tsohon Bango da ya tsatstsage ya rushe, kuma dama yana cikin Bangon da ake aiki akanshi.
Yace, “Ana taba wannan Bangon ne, sai kawai ya rufta, shine ya shafi wasu bangayen”
Sarkin labarai ya kara da cewa, jama a su sani, ba wani abun da ya samu ko wane gini a gidan sarki.
Akan rashin lafiyar Mai Martaba, sarkin labarai yace. Hakika Mai Martaba yaje, an duba lafiyarsa kamar yadda ake yi, akai-akai, Amma yanzu baya Asibiti. Yana zaune a gidansa dake London yana hutawa.
Don haka mutanen katsina su sani Mai Martaba yana nan cikin koshin lafiya. Katsina City News @www.katsinacitynews.com Jaridar Taskar Labarai @www.jaridartaskarlabarai.com The links news @www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245.