…..yadda Alhaji lawal ya rasu
@Katsina City News
Kidnafas din da suka tafi da Marigayi Alhaji lawal tare Malam sabo sun sako Malam sabo.
A ranar lahadi 30/10/2022 suka sako, ya iso gida cikin wahala da misalin karfe shidda na yamma.
Ba kamar yadda aka rika yadawa ba, Cewar an karya masa kafa da bata masa idanu.sam babu ko daya daya same shi.sai dai wayar zama can.
Daga sako shi,an kaishi babbar asibitin katsina inda akayi ta kara masa Ruwa da magunguna.
Malam sabo yace ,kwana hudu da tafiya dasu Alhaji lawal ya rasu a hannun kidnafas din.
Malam sabo ya ce bugu ne, ya kashe Alhaji lawal.yace kidnafas din, sunyi ta bugun shi, wai sai ya fadi ma iyalinsa inda yake boye kudi su dauko su kawo masu.
Wahalar bugu ta kashe shi. Kwanansa hudu a hannun su. Yace duk da ya mutu sun sa anyi masa Janaza an rufe shi.suka ci gaba da maganar kudi da neman a kawo masu kudi.
Malam sabo yana gida yanzu haka yana amsar magani da hutawa.