A wani abinda ba kasafai ya cika faruwa ba Makama Alh. Idris Sule Idris Hakimin Bakori ya shigar da ƙara a kotun Gwamnatin tarayya dake jihar Katsina inda yake neman kotun da ta Hana a ayyana cewa babu Hakimi a Bakori, kazalika kotun ta hana a sanya Sanarwar neman wani hakimi ko kuma a Naɗa wani a matsayin hakimi har sai bayan sauraren wannan ƙarar.
Waɗanda aka shigar cikin wannan ƙarar sun haɗa da Gwamnatin Jihar Katsina, Ƙwamishina Mai kula da ƙananan Hukumomi da Masarautu na jihar Katsina Shugaban ƙaramar hukumar Bakori da kuma Masarautar Katsina.
Idan dai ba’a manta ba a ranar Ashirin da Ukku ga watan Nuwamban Shekarar Dubu Biyu da Ashirin da Biyu ne Masarautar Katsina ta fitar da Sanarwar dakatarwa ga Makaman Katsina Hakimin Bakori inda ta bayyana cewa tana binciken shi akan wasu laifuka, Wanda daga bisani kuma a ranar Goma Sha Tara ga watan Janairu na wannan Shekarar 19/01/2023 Masarautar ta fitar
