Majalisar wakilai ta bayyana bukatar a fara bincike kan jami’an ‘yan sandan da ke kashe mutane babu wani dalili.
Hakazalika, sun bukaci a kawo dokar da za ta haramtawa jami’ai shan giya da sauran kayan maye a fadin kasar nan.
Ana yawan samun lokutan da ‘yan sanda ke kwankwadar barasa a bakin aiki, ko kuma suke kashe mutane babu dalili.
FCT, Abuja – Majalisar wakilai ta kasa na shirin kawo sabuwar dokar haramta shan barasa ga jami’an ‘yan sandan Najeriya da ma sauran dukkan abubuwan maye masu kau da hankali.
Da suke amincewa da kuduruin, ‘yan majalisa sun amince cewa, ya kamata a yi gyara ga dokar ‘yan sandan Najeriya.
Hakazalika, sun yi Allah wadai da yadda wani jami’in dan sanda ya hallaka wata lauya a jihar Legas a ranar kirsimeti, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Wannan batu na gyara dokar dabi’ar ‘yan sanda ta samo asali daga batun gaggawa da dan majalisa Babajide Obanikoro na APC a jihar Legas ya kawo a gaban majalisar a ranar Laraba a Abuja.