Majalisar wakilan Najeriya ta Amince da wani kudiri na gina jami’ar Nazarin Kimiyyar Lafiya a garin Kankia jihar Katsina.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Alhasan Ado Doguwa ne ya gabatar da kudirin domin yimasa karatu na uku aka amince dashi, a yanzu za’akai kudirin ne ga majalisar Dattawa domin itama tayi aikinta akai.
Wanda ya gabatar da kudirin, dan majalisa mai wakiltar Kankia, Kusada da Ingawa Hon. Abubakar Yahaya Kusada ya bayyana cewa idan aka kafa jami’ar zata kasance irinta ta farko a duka fadin Shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya.
Dan Majalisar kuma shugaban kwamitin raba daidai na tarayya a majalisar yace jami’ar zata karfafa koyo da koyarwa a fannonin nazarin kimiyyar Lafiya da nufin karfafa gwiwar tafiyar da Ayyuka a dukkanin ofisoshida sauran cibiyoyin bincike da manyan makarantu masu alaka da nazarin kiwon Lafiya.
Kusada ya kara da cewa jami’ar zata dunga bada gurabun karatu da daukar Aiki bisa la’akari da yardajjin ka’idoji da Dokokin tafiyar da jami’ar na hukumar kula da jami’o,i ta Najeriya.