daga Shafin Rana 24
Majalisar Tsaro ta ƙasa a zamanta na Ranar Alhamis 15/09/2022 da shugaban ƙasa Buhari ta jagoranta, ta haramta ayyukan da wata ƙungiya takeyi mai Ikirarin kula da yadda ake shigowa da ƙananan Makamai a faɗin ƙasar nan wato National Taskforce on small arm and light weapons.
Ministan cikin gida Ra’uf Aregbesola ne ya shelantawa manema labaran dake fadar shugaban ƙasa tare da ministan harkokin Ƴan sanda Mohammed Maigari Dingyadi.
Ya ce a zaman majalisar na yau, majalisar ta jinjina wa aikin da sauran jami’an tsaron ƙasar nan ke yi na tabbatar da tsaro a ƙasar, tare da Bada tabbacin cewa gwamnatin na sa ran ta kawo ƙarshen matsalar tsaro daga nan zuwa watan Disamba mai zuwa.
Majalisar ta kuma gargadi jami’an Taskforce ɗin dake gudanar da wasu ayyuka ba tare da amincewar hukuma ba da su bari ko jami’an tsaro su cafke duk masu aikata hakan.
Shidai ƙudirin ko kundin dokar wannan ƙungiyar yanzu haka ya tsallake karatu na Ukku a majalisar Dattawan Nijeriya inda ta aminta da dokar kirkiro da jami’an tsaron, sai dai lamarin na ci gaba da fuskantar suka daga ɓangarori daban-daban, Ita dai wannan ƙungiya ta Task Force an ɗora Mata alhakkin kula da yadda ake shigowa da ƙananan makamai, da makamai masu guba, gami da kula da masu fasa bututun Man Fetur a faɗin ƙasar nan.
Matasa da dama ne dai aka samarwa da wannan aikin wasu ma sun biya maƙudan kuɗade kafin samun aikin, ko a baya bayan nan ma anga yadda wasu daga cikin ƴan Majalisun Tarayya suke rige rigen samar ma Matasa da wannan aikin da yanzu zamu ce ya zama tarihi.
Koyaya zata kasance ga waɗanda suka biya kuɗin su kafin samun wannan aikin da bayada tabbas Allah Masani.