A zaman majalisar na ranar Litinin biyar ga watan Satumba, majalisar ta amince da karamin kasafin kudi na biyu na shekarar dubu biyu da 2022 ya zama Doka.
Majalisar ta amince da kasafin kudin ne bayan gabatar dashi daga shugaban kwamitin kasafin Ibrahim Umar Dikko, a gaban majalisar domin yimasa karatu na biyu, ansamar da kiyasin karamin kasafin kudin domin samun kammala aikin hanyar Kofar guda, sullubawa zuwa Masanawa a cikin birnin Katsina da zata lashe zunzurutun kudi har naira miliyan dari biyar.
Kudaden gudanar da wannan aiki za a samar dasu ne daga aikin Hanyar Safana zuwa Danmusa da zata wuce Maidabino, inda za a gina hanyar sakamakon matsalar tsaro da ake fuskanta a yankunan.
Har wa yaukuma majalisar ta amince da Naira miliyan Dubu daya da miliyan dari Biyar ga shirin da ake yi na samar da rundunar jami’an tsaro, da zai magance matsalolin tsaro da ake fuskanta, kwamitin ya kuma yabawa wasu kwamitocin majalisar yanda suke ziyartar Ayyuka da ake gudanarwa akai-akai.
Zaman da mataimakin shugaban majalisar dokokin Hon. Sheu Dalhatu Tafoki ya jagoranta, ya umarci akawun majalisar da ya mika matsayar majalisar zuwa majalisar zartaswa.