
A zaman majalisar dokokin na ranar Laraba 21/12/2022, a karkashin jagorancin kakakin majalisar dokokin Rt Hon Tasi’u Musa Mai Gari Zango zauran majalisar ya amince da kasafin kudi.
Amincewa da kasafin kudin ya biyo bayan shawarwarin rahoton kwamitin kasafin kudi a karkashin jagorancin kwamitin Rt. Hon. Aliyu Sabi’u Muduru.
Da sauran mambobin kwamitin su ka gudanar da aiki akan shi tare da gabatar da shi a gaban zauran majalisar.
Bayan gabatar da rahoto, tare da yin karatu na ukku akan kudirin dokar kasafin kudin, daga karshe majalisar ta amince da dokar kasafin kudin na shekara ta 2023.
Inda kakakin majalisar dokokin ya umarci Akawun majalisar daya turawa majalisar zartarwa Jiha domin aiwatar dashi.