Daga Rabiu Ali Indabawa
A ranar Lahadin da ta gabata ce Madarasatu Ummulqura Islamiyya dake Garki a nan Babban Birnin Tarayya Abuja ta gabatar da bikin saukar karatun Alqur’ani Mai Tsarki karo na huxu na a babban Masallacin qasa, taron da ya samu hakartar Malamai, sarakuna, ‘yan siyasa da xalibai
Da yake gabatar da jawabi a yayin gudanar da saukar karatun, wakilin Mininstan Babban Birnin Tarayyar Abuja…… wannan ba qaramin abin farin ciki da alfahari bane a ce yau ga yara sun samu karatun Qur’ani, wanda baiwa ce da ba kowa ne yake samu ba. Ina yi musu murna da fatan Allah ya sanya alheri ya kuma qara musu hazaqa da tsoron Allah.
Shima a nasa jawabin Mataimakin Shugaban Qaramar Hukumar AMAC. Fara godiya ya yi ga Allah da ya basu ikon halartar taron. “ Da farko zan fara gaida uban qasa wato sarkin Hausawan Garki da manyan malamai, iyaye da qanne maza da mata da suka halarci wannan taro mai albarka,” in ji shi.
Ya ce akwai qorafi da babban Malaminmu ya gabatar dangane da matsalar rashin muhalli da wannan makaranta ke fuskanta, da yanayin rashin kyan hanyoyi da kuma yadda za a inganta rayuwar Garki, kuma Allah cikin ikonsa ya sa ya faxa kuma suna kusa. “ Tun da mu ne wakilan jama’a a qaramar hukuma, to Allah ya qaddara Mataimakin shugaban qaramar hukumar AMAC xan Garki ne, kuma in sha Allahu za mu isar da wannan saqo ga qaramar hukuma. Yanzu abin da ya rage shi ne mu haxa kai da ku mu ga yadda za a vullo wa lamarin. Ina fatan Allah ya mayar da kowa gidansa lafiya.
Da yake gabatar da nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Hausawan Garki, Hakimin Garki Hausa Alhaji Umar Abubakar cewa ya yi a madadinsa da iyalansa da kuma ‘yan majalisarsa baki xaya, wannan rana ce da ba za su tava mantawa da ita ba, saboda baiwa da Allah Ta’alah ya yi mana na waxannan ‘ya’ya da jikoki da suka samu saukar Alqur’ani Mai Girima. Alal haqiqa ba mu iyakance farin ciki da godiya ga Allah Ta’alah ga wannan haske da kawo mana,” in ji shi.
Kazalika ya ja hankalin iayaen yara dake yankin da su ci gaba da tura ‘ya’yansu zuwan wannan makaranta domin samun ingantacce ilimin Qur’ani. A qarshe ya yi kira ga masu hanu da shuni da su yi duk mai yiwuwa don ganin sun tallafa wa makarantar domin magance qalubalen da take fuskanta na matsalar rashin isashen muhalli.
Tun da fari a jawabinsa Babban Limamin Masallacin Juma’a na Garki Malam Abdullahi, cewa ya yi sai dai su yi wa Allah godiya game da wannan ni’ima da ya yi musu ta saukar Alqur’ani da yara suka yi.
“Wannan al’amari ba qarfimmu bane ba kuma tarin dukiya makarantar ke da ita ba illa Allah ya sanya albarka a wannan makaranta, muna matuqar farin ciki, domin duk lokacin da aka zo za a yi sauka za ka ga adadin da za su yi sauka a wannan shekarar sun ninka wanda aka yi a baya, da mutum 17 aka fara saukar nan, a gabanka gashi yau xin nan xalibai 62 mun alamtar da cewa sun sauke, kuma daga cikinsu an samu wata yarinya qarama ta haddace Qur’ani, ita ce ta farko da ta haddace Qur’ani a makarantar, sannan nan gaba kaxan za a samu wasu domin suna nan sun kusan kammalawa. Don haka wannan abin farin ciki ne da nuna godiya ga Allah Ta’alah.
“Kuma kamar yadda na fax aba qarfimmu bane ba kuma tara dukiya bane albarka ce daga Allah. Kuma idan ka je aka nuna maka inda Islamiyyar take sai ka yi mamaki,” in ji shi
A qarshe ya yi kira ga al’ummar yankin da su haxe kansu domin kishin kansu da na addini, dmin da haka ne za su samu damar cimma nasarar abin da suka sa a gaba, sannan ya yi addu’ar Allah ya sanya wa yaran da suka yi saukar albarka.
Shi kuwa Shugaban Makarantar ta Ummulqura Isalamiyya Garki, Malam Mu’awiya Idris Salhu, nuna farin cikinsa ya yi da wannan rana ta saukar Qur’an da yara suka yi karo na huxu da Allah ya nuna musu, ya ce a saukar farko da aka gabatar mutum 11 ne, na biyu 25, na uku xalibai 34, yanzu an samu xalibai 62, kuma iyaye na qoqari wajen ganin sun titsiye ‘ya’yansu domin tabbatar da abin da ake koya musu.
Ya ce suna fuskantar qalubale na rashin ajujuwan da za su sanya xalibai don haka ne ya yi kira ga al’ummara yankin da su ba da haxin kai waje ganin an ceto makarantar daga halin da take ciki, saboda babu abin da ya kai ilimi muhimmanci musamman ma na addini.
“ Malaman wannan makaranta na mutuqar qoqari domin xan abin da ake basu bai taka kara ya karya ba, don wani lokacin ma sai dai su fitar daga aljihunsu waje biyan Malaman, ya kamata iyaye su yi hovvasa wajen ganin su kula da neman ilimin ‘ya’yansu. A qarshe ya yi addu’ar Allah ya qarawa malaman makarantar hazaqa.
Mataimakin Shugaban Makarantar kuma xaya daga cikin malamanta, Malam Salihu Adamu Abba, cewa wannan abu ne da ba za ka iya musalta shi ba, domin wannan ba qaramin abin alfahari bane a ce yara sun karance Alqur’ani a wurinka, kuma ba qaramar albarka bace, da yawa dama mutane na neman irin wannan dama amma basu same ta ba, don haka muna cikin murna da farin ciki Allah ya sanya musu albarka.
Xaya daga cikin mamba a kwamitin Yaxa Labarai na wannan makaranta Ummulqura, kuma Jami’in Hulxa da jama’a da yaxa labari Ibrahim Muhammad, cewa ya yi bai san irin farin cikin da yake tare da shi a wannan rana ba, ya yi kira ga iyayen yara da su ci gaba qara wa malaman qwarin gwiwa wajen biyan kuxin makaranta domin su samu sukunin koyar da xaliban.
“ Idan ka duba kuxin da muke sayen katin da muke Data a wayoyinmu ya isa a ce mun dawo hayyacimmu mun taimaka wa ‘ya’yanmu wajen samun ingantaccen ilimi.
Wasu daga cikin xaliban da suka yi nasarar saukar, kamar Ibrahim, Mubarak B. Muhammad, Isma’il Isa, Bashir Abdullahi, Mufida Sufyan, Maryam Muhammd, addu’a suka yi ga iyaye da malamansu bisa ga wannan qoqari da suka na basu ingantaccen ilimi