
A ci gaba da Taron Kimiyya karo na 62, haɗi da Babban Taron Shekara na Ƙungiyar Likitocin Fisiyoterafi ta Najeriya, an ɗaga likkafar wasu ƙwararrun likitocin fisiyo zuwa matsayin kwanzalta a ƙarƙashin Babbar Kwalejin Fisiyoterafi ta Najeriya.
Ɗaga likkafar tasu na zuwa ne yayin da ake ci gaba da gudanar da taron wannan shekara ta 2022 a Cibiyar Taro ta Amadeo, a jihar Enugu. Taron da aka fara gudanarwa tun ranar 9 ga watan Oktoban nan wanda kuma ake sa ran ƙarƙare shi a ranar 15 ga watan Oktoban.
Sashin Fisiyoterafi na Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH), da ke Kano, ya samu ƙarin kwanzaltoci uku wanda suka haɗa da:
- Dr. Abdullahi Sule Dambatta (PT), FPPCN, Kwanzaltan Zuciya da Huhu.
- Dr. Maryam Abdulhadi (PT), FPPCN, Kwanzaltan Ƙashi da Raunukan Wasanni.
- Dr. Rukayya Ibrahim Hassan (PT), FPPCN, Kwanzaltan Lafiyar Mata.
Masana likitancin fisiyoterafi daga ciki da wajen ƙasar nan ne ke ci gaba da gabatar da muƙaloli da ƙasidu a ɓangarorin ƙwarewa na fisiyoterafi daban-daban a babban taron.