Wata kotun laifuffuka ta musamman da ke Ikeja, karkashin jagorancin mai shari’a Mojisola Dada ta yanke wa wani makaneza, mai suna Chidozie Onyinchiz ɗan shekara 32 hukuncin kisa ta hanyar rataya a yau Talata, bisa laifin yi wa wata ma’aikaciyar lafiya fashin Naira dubu 57.
Mai shari’a Dada ya bayyana cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da tuhume-tuhume uku na hada baki, fashi da makami da kuma zama mamba na wata haramtacciyar ƙungiya a kan Onyinchiz.
Dada ta ce yunƙurin da mai laifin ya yi na murƙushe tuhume-tuhumen bai yi nasara ba.
Ta ce hakan ya faru ne saboda tun da farko ya tabbatar wa ‘yan sanda a Igando da ke Legas cewa wacce ya yi wa fashin, Misis Veronica Uwayzor ta gan shi kuma dukkansu sun gane juna a lokacin da aka aikata laifin.
“Wanda ake tuhumar ya bayyana cewa wacce ta shigar da karar ta nuna shi a matsayin daya daga cikin yaran dauke da almakashi kuma ya kwace jakarta da karfin tsiya mai dauke da kuɗi N57,000 a tashar motoci ta Akesan.
“Mai shigar da karar ta bayyana cewa wanda ake kara, da abokin aikata laifin, Ediri Endurance, (ya tsere) ba su sanya abin rufe fuska ba a lokacin aikata fashin, wanda hakan ya sa ta samu saukin gane Onyinchiz bayan ‘yan sa’o’i da fashin.
“Irin wannan bayanin nasa na vulcanis din yana kunshe ne a cikin bayanan da ya yi a ofishin ƴan sanda na Igando da kuma wanda ya yi a ofishin ‘yan sanda na musamman da ke yaki da ‘yan fashi da makami da ke Ikeja.
“A cikin bayanan da ya bayar na ikirari, Onyinchiz ya bayyana cewa ya hadu da Ediri Endurance a cikin wata motar bas ta haya, kuma Endurance ta kai shi gidan su bayan motar ta samu matsala.
“Ya kuma bayyana cewa a wani kango su ka kwana saboda mahaifin Endurance bai bude musu kofar gidan ba.
Jimillar shaidun da ke gaban kotu suna da karfi kuma na sami wanda ake tuhuma da laifin da ake tuhumarsa da shi.
“An yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya kuma Ubangiji ya jikansa da rahama,” in ji Mai shari’a Dada.