Labari Mai dadi, dake zo mana shine, Gamayyar jami an tsaron sojaji, yan sanda, jami an DSS da taimakon yan sintiri, sun kai daukin Gaggawa a inda Barayin suke tattaruwa a dajin Barawa da kuma yankin kwarin Bugaje.
Majiyarmu a jami an soja,tace tun farkon dare da bayanai suka zo na tattaruwar su.Gwamanna katsina ke ta magana da hukumomin tsaro da Kan shi.
Wannan magana ta gwamnan, ya Sanya, hatta sojan sama sun tayar da wani jirgi yana shawagi cikin daren nan
A Dajin Barawa, barayin sun bar wasu mashinan su a inda suka taru saboda tsoro.
A kwarin Bugaje ,,barayin sun guda sun nusa cikin daji daga inda suke tattaruwa.
Wasu mutanen kauyukan yankin Babbar Ruga sun tabbatar ma jaridun mu cewa.An gansu a kasa suna tafiya cikin sanda da sunji motsi sai su lahe.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com