Kociyan tawagar kwallon kafar Najeriya, Jose Santos Peseiro ya gayyaci ‘yan wasa 23, domin buga wasan sada zumunta da Algeria.
Ranar Talata 27 ga watan Satumba, Super Eagles za ta fafata da Algeria a Oran.
Cikin ‘yan kwallon da aka bai wa goron gayyata har da kyaftin din tawagar, Ahmed Musa da mataimakinsa, William Ekong.
Ranar Litinin 19 ga watan Satumba ake sa ran ‘yan wasan da aka gayyata za su ziyarci Constantine, domin fara atisayen tunkarar mai rike da kofin nahiyar Afirka karo biyu a tarihi.
Jerin ‘yan kwallon da aka bai wa goron gayyata
Masu tsaron raga: Francis Uzoho, Maduka Okoye da kuma Adeleye Adebayo.
Masu tsaron baya: William Ekong, Kenneth Omeruo, Chidozie Awaziem, Olaoluwa Aina, Calvin Bassey, Zaidu Sanusi, Kevin Akpoguma da kuma Leon Balogun.
Masu buga tsakiya: Wilfred Ndidi, Frank Onyeka, Alex Iwobi da kuma Richard Onyedika
Masu cin kwallaye: Ahmed Musa, Kelechi Iheanacho, Moses Simon, Samuel Chukwueze, Ademola Lookman, Henry Onyekuru, Taiwo Awoniyi, Chidera Ejuke, Cyriel Dessers da kuma Terem Moffi.