Tsohon gwamnan Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce babu gaskiya a batutuwan da jagoran jam’iyyar NNPP kuma ɗan takarar shugaban kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso ke yi cewa sun shigo jam’iyyarsa a makare.
Sanata Shekarau a wata hira da ya yi da BBC bayan taron majalisarsa ta Shura a Kano, ya ce har yanzu suna kan tattauna da tuntubar juna domin sanar da matsayarsu kan ci gaba da zama a NNPP ko akasin haka.
Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa Malam Shekarau na gab da sauya Sheka zuwa PDP.
Sai dai duk da cewa Malam Shekarau bai ambaci ko tabbatar da jam’iyyar da zai koma ba idan ya sauya sheka, a hirar da BBC ta yi da shi ya nuna rashin jindadinsa kan hanasu wasu muƙamai da kuma hana magoya-bayansa damar takara a NNPP.
ce taron da sukayi a wannan rana amsa ce ta abin da kwankwaso ke cewa sun shigo jam’iyyar a makare. Saboda tun kafin su shiga jam’iyyarsa akwai yarjejeniya da aka cimma har kafa kwamiti aka yi.
‘Ni kaɗai aka bai wa takara a NNPP’
A makon da ya gabata ne Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya shaidawa BBC cewa hukumar zabe ta INEC ta rufe karbar sunayen ‘yan takara lokacin da ɓangaren shekarau suka gabatar da bukatunsu na takara.
Kwankwaso ya ce wannan dalili ne ya sa aka yi musu wasu alkwarin wasu mukamai idan sun yi nasara a zaɓen 2023.
Sai dai Malam Ibrahim Shekarau ya ce sun gabatar da bukatunsu ga Sanata Kwankwaso watanni uku kafin cikar wa’adin da INEC ta bayar na daina karbar sunayen ‘yan takara.
Ya ce tun a ranar 16 ga watan Mayun 2022, aka kafa kwamitin da aka bai wa wa’adin kwanaki uku su gabatar da rahotonsu amma sai suka shafe wata uku babu labari, duk da kokarin da ɓangarensa suka rinka yi domin cimma lokaci.
Malam Shekarau ya ce bayan shi da aka bai wa takara sauran mutane da suka koma NNPP tare babu wanda ya samu wani tiketin.
Shekarau ya ce babu mamaki kwamitin da aka nada karkashin ɗan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar, Abba Kabiru Yusuf, su suka rinka jan kafa.
A cewarsa har rugawa ya yi Abuja domin tattaunawa da Kwankwaso amma babu wani abin da ya sauya.
‘Babu tsamin dangantaka tsakani na da Kwankwaso’
Sanata ya jadada cewa akwai kyakyawar alaƙa tsakaninsa da Kwankwaso, babu rashin jituwa ko wata matsala tsakaninsu.
Sai dai duk abin da zai yi dole ya ke duba bukatun mutanensa.
Sanatan ya ce wadannan batutuwa su suka sanya majalisarsa ta shura ke laluben mafita, kuma tuni suke ta samun gayyata daga jam’iyyu daban-daban na Kasa.
Kuma a cewarsa nan da ‘yan kwanaki kadan za su tabbatarwa al’umma matsayarsu.