Liz Truss ta sanar da yin murabus daga mukaminta na Firaministar Birtaniya bayan da ta shafe kwanaki 44 tana mulki a cikin rudani, inda ta rasa amincewar Æ´an majalisar dokokinta na jam’iyyar Conservative, da Æ´an majalisar dokoki, da kuma jama’a ga kuma tarzomar tattalin arziki.
Za ta zama firaminista mafi karancin wa’adi a tarihi bayan da ta sha fama da adawa daga jam’iyyar Conservative da ke neman ta yi murabus.
Da ta ke magana daga wata lacca a Downing Street a yau Alhamis Truss ta ta gaya wa Sarki Charles III cewa ta yi murabus a matsayin shugabar jam’iyyar Conservative saboda ta fahimci cewa “ba za ta iya sauke nauyin ” da mambobin Tory suka ba ta makonni shida da su ka gabata.
Ta yi tattaunawa da shugaban kwamitin 1922 na Conservatives, Graham Brady kuma ta amince da sabon zaÉ“en jagoranci “wanda za a kammala a cikin mako mai zuwa.”
Ta kara da cewa, “Wannan zai tabbatar da cewa mun ci gaba da kasancewa a kan hanyar da za mu bi don isar da shirin kasafin kudinmu da kuma kiyaye zaman lafiyar kasarmu da tsaron kasa,” in ji ta, yayin da take tare da mijinta Hugh O’Leary.
“Zan ci gaba da kasancewa a matsayin Firayiminista har sai an zabi wanda zai gaje ni”
Shugaban jam’iyyar Labour Keir Starmer ya bukaci a gudanar da babban zabe “yanzu” domin al’ummar kasar su samu “dama a sabuwar gwamnati.”
Murabus É—in nata ya zo ne bayan sa’o’i 24 bayan da ta gaya wa Æ´an majalisar cewa “mai gwagwarmaya ce, ba mai karaya ba.”