Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Jam’iyyar APC mai mulki, APC, na nan na kaddamar da wata manhaja ta Crowdfund App, da nufin tara kudade don tallafa wa yakin neman zaben dan takarar ta, Bola Tinubu da Mataimakin takararsa, Sanata Kashim Shettima a yau Talata.
An shirya kaddamar da app din wanda ya gudana a Cibiyar Civic Centre, titin Ozumba Mbadiwe, Victoria-Island da karfe 11 na safe.
Gwamnan jihar Legas, Bababjide Sanwo-Olu, ya jagoranci sauran manyan baki a wajen taron
Majalisar ta yi bayanin cewa app din zai baiwa ‘yan Najeriya damar yin zaben adadin kudaden da za su iya bayar wa na tallafi ga Tinubu.
Kwamitin ya ce “Tara kuɗin zai baiwa jama’a damar rage tasirin siyasar kudi, da baiwa ‘yan kasar da dama fahimtar zama tare da zurfafa dimokiradiyya a kasar.”