Bayan sauke mahaifinta daga sarautar Wazirin Bauchi, Kwamishinar harkokin ƙananan masana’antu ta jihar Bauchi, Hajiya Sa’adatu Bello Kirfi, ta yi murabus daga mukamin ta.
A wasiƙar ajiye aiki da ta rubuta mai ɗauke da kwanan watan yau Laraba 4 ga watan Janairu, Kirfi, ta bayyana godiyar ta ga gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir bisa ba ta damar yin aiki a ƙunshin gwamnatin sa.
Sai dai tsohuwar Kwamishinar ba ta bayyana dalilin ta na yin murabus ba.
Sai dai kuma Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa an tuɓe rawanin mahaifin kwamishinar bisa zargin rashin biyayya ga gwamnan jihar.
A wasikar, kwamishinar ta ce, “Mai girma gwamna, ina mai miƙa takardar murabus ɗina daga matsayin mamba ta majalisar zartaswar jihar Bauchi kuma kwamishina a ma’aikatar Gama Kai da Kananan masana’antu ta jihar Bauchi nan take.
“Ina son gode wa mai girma gwamna bisa damar da ya bani na yin aiki a karkashin gwamnatinsa.” cewar sanarwar.