Katsina Youth Coalition Group sun Karrama Mai taimakawa Gwamnan jihar Katsina akan wayar da kai S.A Abdul’aziz Mai Turaka. Karramawar tazo daidai da lokacin da Cibiyar koyar da Sana’o,i ta MD Yusuf Katsina Vocational Training Centre KVTC, take Yayen Daliban da ta horas akan sana’o,i daban-daban da basu Tallafin jari domin dogaro da kai. Da yake jawabi game da dalilin Karramawar Shugaban cibiyar KVTC Malam Danjuma Katsina ya bayyana irin gudummawar da Mai Turaka yake bayarwa domin tallafawa masu koyan Sana’o’in a duk Lokacin da bukatar hakan ta taso, yace a shekarar bara S.A mai Turaka ya bada gudunmawa mai tsoka, a bana ma ya sake badawa, inda ya zabi kananan hukumomi biyar ya tallafawa Mutum goma-goma da jari, yace Kungiyar KCYG ta yaba kokarin sa shiyasa ta zabeshi domin karramawa kuma don koyi ga ‘yan baya.
Abdul’aziz Mai Turaka ya yaba da nuna jin dadinsa game da wannan karamci da Gamayyar Kungiyar Matasan tayi masa. Sana yayi jan hankali akan muhimmancin biyayyar Iyaye, yace: “Duk wani cigaba da na samu na rayuwa to Albarkar biyayyar Iyaye ce, kuma ina fatan duk wani Aiki da nayi na Alkhairi Allah yakai Ladar ga mahaifiyata.” inji mai Turaka. A karshe ya yabawa Gwamnatin Aminu Masari akan yanda ta muhimmantar da samar da Ilimi da bawa sana’o’i muhimmanci domin dogaro da Kai.
