Ƙungiyar Malaman tsangaya mai suna “Tsangaya Morden School” ta ƙasa reshen Jihar Katsina, a ƙarƙashin jagorancin Gwani Masa’udu Rafin-daɗi, ta gudanar da Safkar Qur’ani mai girma sau 313 da gudanar da Addu’o,i na Musamman don samun Zaman lafiya a jihar Katsina.
Da yake jawabi a wajen taron addu’a da aka rufe a makarantar Firamare dake Unguwar Kofa uku, Sakataren Ƙungiyar Malam Ɗahiru Filin Bugu ya bayyana maƙasudin gudanar da Addu’o,in cewa, “Mun shirya waɗannan Safkokin Alqur’anin ne domin ganin halin da jihar Katsina ta shiga, muna neman zaman Lafiya, muna neman sauƙin Rayuwa, don haka bamu da wani gata sai Allah, shiyasa muka maida al’amurrammu gareshi domin samun mafita.” Injishi
Gwani Masa’udu Rafin-daɗi Shugaban Ƙungiyar ya bayyana Yanda ƙungiyar ta samo Asali da kuma hadafinta, inda yace “Muna so mu samar da gagarumin haɗinkai domin maganin wasu matsaloli da suke faruwa a cikin tsangayun mu, ba zamu taɓa iya magancesu ba sai mun samar da kyakkyawan haɗin kai, kuma mun cire hassada ganin ƙyashi.” Inji Gwani Masa’udu.
Sana kuma ya bayyana cewa, sunyi ne don Allah don kishin ƙasa da jihar Katsina, babu wani dan Siyasa ko mai Mulki da ya basu ko sisin Kwabo domin gudanar da wannan taron Addu’o, i.
Sheikh Haruna Bakin gi-da, yana ɗaya daga cikin Shehinnai da suka gabatar da Addu’a da kuma tsokaci a wajen taron.
Sheikh Abdulwarsi daga Ƙaramar Hukumar Daura ya faifaye gami da jawabi mai ratsa zukata akan Haɗinkan Al’ummar Musulmi, da kuma Manufofin ƙungiyar, sana ya ja hankalin ‘Ya’yan ƙungiyar akan shirya da’awa a Lungu da saƙo na jihar Katsina domin ta hakan zaisanya Ilimi ya yaɗu.
Sheikh Ɗayyabu Liman, (Ratibi) ya yi nasiha da Addu’a ga wadanda suka shirya wannan taro, sana ya jaddada goyon bayansa ga ‘Ya’yan ƙungiyar a matsayin sa na Uba kuma Malamin da ya koyar da ɗaliban da suka Assasa ƙungiyar.
Malamai Alarammomi ne daga ciki da wajen Katsina suka halarci taron.