Shahararriyar Kungiyar Nan Mai Yaɗa Manufofin Da Kuma Ganin Jam’iyyar PDP Ta Samu Nasarar Lashe Zaɓen 2023 A Kowane Matakai Watau Ladon Alkhairi Ƙarƙashin Jagorancin Darakta Janar Na Ƙungiyar, Honarabul Musa Yusuf Gafai Ta Naɗa Hazikan Matasan Da Su Jagoranci Yaɗa Manufofin Ƴan Takarar Jam’iyyar PDP A Jihar Da Kuma Kasa Baki Ɗaya.

Bayanin Hakan Na Kunshe A Cikin Wata Takardar Manema Labarai Da Darakta Janar Na Ƙungiyar Honarabul Musa Gafai Ya Sanyawa Hannu Aka Rabawa Manema Labarai A Katsina Yau Alhamis.
A Cikin Takardar An Zakulo Matasa Ashirin Da Takwas Da Za Su Jagorancin Yaɗa Manufofin Da Kuma Tallata Ƴan Takarar Jam’iyyar PDP A Kowane Kuma An Naɗa Umar Tukur Gafai A Matsayin Shugabanta. Kuma An Naɗa Shugabannin Shiyyar Dan Majalisar Dattawa Na Daura Da Katsina Da Kuma Shiyyar Funtua.
Kungiyar Ladon Alkhairi Ƙarƙashin Jagorancin Honarabul Musa Gafai Ta Amince A Kira Wannan Bangare Na Yaɗa Manufofin Jam’iyyar PDP Da Sunan (Ladon Alkhairi Media Reporters)