A ranar Litinin kungiyar yakin neman zabe ta Sanata Yakubu Lado Danmarke mai suna “Ladon Alkhairi” ta Kaddamar da wani bangare na masu fafutukar tare da Tallata Dantakarar Gwamna da jam’iyyar PDP a jihar Katsina. Wato (Ladon Alkhairi Media Repoters)
Da yake jawabi a wajen taron kaddamarwar mai taiamakawa Ɗantakarar Gwamna Lado Danmarke akan kafafen sada Zumunta, Hon. Babangida Kayawa ya bayyana jin dadinsa da nuna goyon bayansa dari bisa dari da kuma tabbatar masu cewa a matsayin sa na mai taimakawa Lado a akan kafafen sada zumunta, zasuyi tafiya kafada da kafada da su. Sana kayawa ya basu gudumawar Naira dubu hamsin domin su sha Data. Shugaban PDP Social Media na jihar Katsina Comrade Nura Tina ya basu shawarwari akan yanda zasu inganta aikin nasu, sana yace sunada Abin talla, kada suji shakkar bayyana hajarsu, yace Lado da duk wani wanda PDP ta fitar masu nagarta ne.
Bayan gabatar da dukkanin ‘yan Social Media da mikamasu shedar kama Aiki, Hon. Musa Gafai shugaban kungiyar Ladon Alkhairi Hon. Gafai ya tabbatar masu da cewa lallai kungiyar Ladon Alkhairi zata sanya masu ido sosai kuma ba zatayi wasa da aikinsu ba, yace kune jigon tafiyar Ladon Alkhairi, kuyi aiki tsakanin ku da Allah banda cin mutumci, banda kage, banda yin Rubutu maras ma’ana idan zakuyi rubutu kusan abinda zaku rubuta. Ya kara da cewa duk wani dantakara da kuke so kuyi Fira da shi yace kuyi mana magana zamu hadaku dashi.” Inji Gafai
Kafin nan Sakataren Kungiyar ta Ladon Alkhairi Abubakar ‘Yantaba yayi dogon jawabi da jan hankali gami da kara sanar dasu yanda zasu Tallata ‘Yantakararsu.
Wadanda aka bawa mukamin sunfito daga kananan hukumomin 34 na jihar Katsina da shiyyoyi 3 na jihar, inda kuma aka basu umarni da su tafi su fara shiri saboda za a fara yakin neman zabe. A karshe musa Gafai ya sanar dasu zai basu Mota ta Aiki da kyamarori na Aiki.