
Kungiyar, ta yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da Dikko Umar Raɗɗa a ƙarƙashin Inuwar Jam’iyyar APC wadda Ibrahim Kabir Masari ke jagoranta, a ƙarƙashin kulawar Alhaji Aliyu Ilu Barde, ta tallafawa wata mata da mijinta ya Mutu ya barmata Marayu mata a gabanta kusan watanni goma sha ɗaya a yanzu.
Hajiya Binta Uwar gida ce ga Mariganyi Alhaji Sada, da Allah yayiwa rasuwa a shekarar bara, sanadin gajeruwar jinya, ya rasu ya bar Matarsa da ‘ya’ya biyar (Mata) da suke cikin bukatar Tallafi. A sakamakon haka ne kungiyar nan ta Yaƙin neman zaɓen Bola Ahmed Tinubu da Gwagwaren Katsina, wacce ta saba bada tallafi ga mata da masu ƙaramin karfi a ƙarƙashin jagorancin Tsohon Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, Ibrahim Kabir Masari bisa kulawar Alhaji Aliyu Ilu Barde. Ta binciko tare da kaima Hajiya Binta da ‘Ya’yanta gudumawa da zai taimaka mata don rage wata hidimar.
Da yake jawabi a yayin gabatar da gudumawar, Malam Lawal Ummaru ya bayyana maƙasudin zuwa da kuma gabatar da ita gudunmawar kuɗin ga hajiya Binta, inda yace “Koda yake ƙungiya ce ta Siyasa, amma yanzu mu ba Siyasar ta kawo mu ba, munzo ne akan irin ayyukan da ƙungiyar ta saba na taimakon marasa ƙarfi, da kuma marasa lafiya.” Yace “to balle ku zamu iya cewa kamar Tallafi ne na cikin gida, saboda Mijinki munsanshi mutumin kirki ne da bashi da abokin fada.” Malam Lawal ya bayyana muhimmancin yada Alkhairi a tsince shi a gaba.
Yace lallai mijinki ya yada Alkhairi ne, sakamakon hudda ta Arziƙi da akai dashi, kuma shi Alhaji Aliyu yasan haka shi yasa ma yace lallai zai bada wani ihisani a kawo don saima yara koda Litattafan Makaranta, shine ya bada a kawo maki da yaranki. inji shi
Hajiya binta ta yaba matuka da kuma Addu’ar Fatan Alkhairi ga wannan ƙungiya da jagoran tafiya, gami da yi masa Addu’a akan niyyoyinsu na Alkhairi. Kwamitin ya samu rakiyar wani na hannun damar jagoran kungiyar, wato Jamilu Labour da sauran ‘Yan kwamiti