Kungiyar Izala tayi kira ga Limamai da Malamai da sauran al’umar Jihar Katsina su dinga sanya Sarkin Katsina Alh. Dr. Abdulmumini Kabir Usman cikin addu’a
Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah na Jihar Katsina, Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Katsina (Sautus-Sunnah) yayi kira da bada umarni ga Limamai da Malamai akan sanya Sarkin Katsina Alh. (Dr.) Abdulmumini Kabir Usman a cikin addu’a akan jinyar da yake ta rashin lafiya
Sheikh Sautus-Sunnah yayi wannan kirane a wajen taron lakcar da ta gudana da yammacin ranar Lahadin da ta gabata a Masallacin Juma’a na Moddibo (Khandahar) Kofar Kaura Katsina wadda Dr. Adamu Ahmad Bunkau ya gabatar
Haka kuma Sheikh yayi kira da a kara sanya Kauran Katsina Hakimin Rimi Marigayi Alh. Nuhu Abdulkadir wanda Allah (S.W.A) yayi ma rasuwa a satin da ya gabata
Muna rokon Allah ya ba Mai Martaba Sarki lafiya, ya sanya kaffara ne ya kuma dawo mana da shi lafiya
Marigayi Kaura kuma Allah ya jikanshi, ya gafarta ma shi, ya kyautata makwancinsa. Mu kuma idan ajalin mu yayi ya sanya mu cika da Imani. Amin
JIBWIS Katsina
02 Safar, 1444
30 August, 2022