
Kungiyar nan ta Siyasa mai suna ‘Dan Guruf Support For Tinubu 2023’ ta ziyarci Jigon siyasa a Katsina, Honorabul Hamisu Gambo.
Ziyarar wadda ta gudana da yammacin ranar Lahadin nan, ta samu halartar dimbin magoya baya ‘yan amana na kungiyar, wadanda suka hada da maza da mata.
A lokacin da yake jawabin makasudin ziyarar, Ciyaman na kungiyar Alhaji Ghali Yusuf ya bayyana cewar ziyarar na da manufar ziyarar gaisuwa da ban girma ne ga jigon siyasa Hamisu Gambo Dan Lawan Katsina, da kuma samun shawarwarin siyasa domin jam’iyyar APC ta cimma nasara a za6ukan 2023.
A yayin da yake jawabin kar6ar ziyarar, Honorabul Hamisu Gambo wanda ya dawo jam’iyyar ta APC a cikin satin nan, ya bayyana gamsuwarsa da wannan kungiya ta ‘Dan Guruf Support For Tinibu 2023’ tare da shan alwashin aiki da ita kafada-da-kafada domin kai jam’iyyar APC a nasara a za6en Shekarar 2023.
Hakazalika, Dan Lawan Katsina ya bayyana cewar za suyi duk mai yiwuwa don kawo dukkan kujerun ‘yan takarkari a jam’iyyar ta APC za6en da yake gabatawa.
