Da sanyin Safiyar ranar juma’a ne Kungiyar Yaƙin neman zaben Ɗantakarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Bola Ahamed Tinubu suka tarbi tawagar ɗan takarar Gwamnan jihar Katsina Dakta Dikko Umar Raɗɗa da manyan Banonin da Alluna masu dauka da Hotunan ‘Yan takarar na ƙasa da na jihar Katsina, masu alamta goyon baya ga APC daga sama har ƙasa.
Ƙungiyar ta Ɗan Guruf Support for Tinubu 2023 da Alhaji Masa’udu Abdulƙadir Dan Guruf kuma shugaban sashin wayar da kan jama’a da tuntuɓa, na kwamitin yaƙin neman zaben Bola Tinubu a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, tana ɗaya daga cikin kungiyoyin da ke shiga lungunan jihar Katsina domin taya ɗan takarar Gwamnan jihar Katsina Dakta Dikko Radda yakin neman zaben sa na 2023.
Source:
Katsina City News
Via:
Katsina City News