Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’in Nijeriya ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta kwashe watanni takwas ana yi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Duk da cewa kungiyar ba ta fitar da sanarwar a hukumance ba, kungiyar ta cimma wannan matsayar ne a karshen taron majalisar zartarwa ta kasa da aka gudanar a sakatariyar ASUU da ke Abuja.
Wata majiya daga Majalisar Zartarwar ASUU, ta tabbatar da janye yajin tare da bayyana cewa Shugaban Kungiyar na kasa zai fitar da sanarwa a hukumance a safiyar Yau Juma’a.
Kungiyar ta ASUU ta fara yajin aikin ta ne tun a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu, 2022.
Source:
Taskar labarai
Via:
Zaharadeen