Kungiyar nan ta yaƙin neman zaɓen Bola Ahamed Tinubu da Dakta Dikko Umar Raɗɗa, a jihar Katsina mai suna Asiwaju Gwagware gida-gida ta Alh. Ibrahim Masari, ƙarƙashin jagorancin Hon. Aliyu Ilu Barde taci gaba da rabon kayan tallafi da take a garin Katsina.
Tallafin da zai karaɗe Gidajen Marayu, Tsangayu da Gidajen Marasa galihu, zasu samu Tallafin Tabarmi, guda dubu 5, Butoci Dozin dubu 5, Bargunan Rufa, da Shadda Bandir dubu biyar a faɗin jihar Katsina. A yau Alhamis Jagororin Kungiyar sun Dira Unguwar Unwala, inda suka bada Tallafin.
Hon. Aliyu Ilu Barde ya bayyana cewa amfara da ƙaramar Hukumar Katsina ne, wanda daga bisani zaka ƙetara wasu ƙanan hukumomin.
Source:
Katsina City News
Via:
Katsina City News