Babbar kotun tarraya da ke zama a Umuahia babban birnin jihar Abia ta bukaci gwamnatin Najeriya ta biya shugaban kungiyar ‘yan aware na IPOB naira miliyan 500 a matsayin diyya.
Mai shari’a Evelyn Anyadike ce ta yanke hukuncin a zaman kotun na yau kan shari’ar da Kanu ya shigar a kan cewar an tilasta dauko shi daga kasar Kenya zuwa Najeriya a watan Yunin 2021, inda ya ce hakan ya saba ka’ida.
A watan Maris ne, lauyoyin Kanu suka shigar da karar a kan cewa matakin gwamnatin Najeriya na dauko shi daga Kenya ba tare da yardarsa ba, an keta masa ‘yancinsa.
Kawo yanzu babu martani a hukumance daga wajen gwamnatin Najeriya a kan wannan shari’ar ta yau.
Makonni biyu da suka wuce, kotun daukaka Æ™ara ta Najeriya ta yi watsi da dukkan tuhume-tuhumen da ake yi wa madugun ‘yan awaren, Nnamdi Kanu a wata shari’ar ta daban da aka yi.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce watsi da karar ba yana nufin a saki Kanu daga kurkukuba ne, kuma a cewar gwamnatin akwai shari’u daban-daban da ke tsakaninta da shugaban na IPOB.