Nan gaba kaɗan ne yau a Najeriya ake sa ran kotu za ta yanke hukunci kan buƙatar da wasu jam’iyyun adawar ƙasar suka shigar gabanta suna neman a ba su damar duba kayayyakin da aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasar da su, ranar 25 ga watan jiya.
‘Yan takarar jam’iyyun adawa na PDP Atiku Abubakar da na LP Peter Obi ne, tare da zaɓaɓɓen shugaba ƙasar Bola Ahmed Tinubu ne suka buƙaci kotun da ta tilasta wa INEC adana kayayyakin da aka gudanar da zaɓen da su gabanin shigar da ƙara don ƙalubalantar sakamakon zaɓen, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.
To sai dai hukumar zaɓen ƙasar ta buƙaci kotun da ta ba ta damar sake saita na’urorin BVAS gabanin zaɓen gwamnoni da za a yi ranar 11 ga watan Maris.
INEC ɗin dai ta sha alwashin yin amfani da na’urar BVAS a zaɓukan na gwamnoni da ke tafe a ƙarshen makon da muke ciki.
Jam’iyyar PDP ta ce buƙatar da INEC ta gabatar na sake saita na’urorin, ta yi shi ne da nufin goge cikakkiyar shaidar sahihancin zaɓen da ke ƙunshe cikin na’urorin.
Hukumar zaɓen ƙasar INEC dai ta sha suka, a gefe guda kuma ta sha yabo kan zaɓen shugaban ƙasar da ta gudanar, wanda masu sanya idanu suka ce yana cike da matsaloli na shirin hukumar da rashin gudanar da komai a bayyane.