Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da hukuncin da ya samu shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa da laifin raina kotu.
Mai shari’a Chizoba Oji ce ta ya yi watsi da hukuncin a ranar Alhamis, bayan sauraron ƙorafin da shugaban hukumar yaƙi da rashawa da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati ya shigar.
Kotun ta ce ta gano cewar ba za a iya cewa shugaban na EFCC ya raina kotu a lokacin da aka yanke hukuncin ba, kasancewar ya riga ya bayar da umurnin a mayar wa wanda ya shigar da ƙarar motarsa ƙirar Range Rover.
Kotun ta ce takardu sun nuna cewa an fara shirin mayar wa mai ƙorafin motarsa da kuma kuɗi naira miliyan 40.
A ranar Talata ne mai shari’a Chizoba Oji ta yanke hukuncin cewar EFCC ta raina kotu ta hanyar ƙin bin umurnin hukuncin da ya ce a mayar wa wani mutum motarsa da kuma kuɗi naira miliyan 40.