Kotun majistare dake a Kaduna ta yanke wa Nasiru Yusuf da Tijjani Idris da ake zargi da laifin sace bokatan fenti shida a wani shago hukuncin biyan beli har naira 100,000.
Yusuf mai shekaru 28 da Idris mai shekaru 24 na zama a kauyen Kinkinau ne dake Kaduna.
Dan sandan da ya shigar da karar Chidi Leo ya ce Wani Aliyu Shugaba mazaunin titin Ahmadu Bello way ne ya kawo kara a ofishinsu dake Gabasawa ranar 15 ga Afrilu.
Leo ya ce Shugaba ya bayyana cewa Yusuf da Idris sun kutsa shagonsa dake titin Taiwo road a Kaduna suka sace bokatan fenti shida da janareta daya duk da aka yi musu kudi naira 185,000.
Ya ce Shugaba ya Kuma ce barayin sun saci kofofi guda biyar, katan biyu na tiles din bango da katan biyu na tiles din kasa duk da aka yi musu kudi akan naira 235,000.
Leo ya ce masu gadin wurin ne suka kama barayin
Sai dai kuma Yusuf da Idris sun musanta aikata laifin da ake zargin su da shi.
Alkalin kotun Ibrahim Emmanuel ya bada belin kowanen su akan naira 100,000.
Emmanuel ya ce kowannen su zai gabatar da shaida daya da zai nuna da shaidan biyan gwamnatin jihar Kaduna haraji.
Za a ci gaba da shari’ar ranar 28 ga Yuni.