TSAKA MAI WUYA:
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce babban abin baƙin ciki shi ne a ce sun rasa Kano, amma yace dole laifin wasu ne yasa suka faɗi zaɓe a Kano, saboda son zuciya irin tasu.
Ya ce, “ Kamar Kano, a ce mun rasa Kano, to amma laifin wasu ne ya sa muka fadi a Kanon.”
Shugaban na APC, ya ce “ Akwai wadanda ba su yi abin da ya kamata ba, ga shi a yanzu ya sanya ‘ya’yan jam’iyar cikin wani hali saboda nasarar da jam’iyyar ba ta samu ba, bayan ga shi su sun yi duk abin da ya kamata su yi.”
Sashen Hausa na BBC ya rawaito cewa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce Kano tana cikin jihohin da suke bugun kirji su ce wannan tamu ce, domin duk abin da za su yi Kano na kan gaba a lissafinsu.
Ya ce, “ Saboda wasu abubuwa na son zuciya an samu a cikin wani hali domin bai kamata a ce mun rasa Kano ba, to amma duk abin da ya samu bawa da sanin Ubangiji.”
“Sai da muka ja dukkanin gwamnonin jam’iyyar APC a jihohin Najeriya a kan a rage son zuciya tun kafin zabe, kuma muna ganin son zuciyar ne ya ja mana rashin nasara a jiha kamar Kano,” In ji shi.
Shugaban APCn, ya ce yanzu jira suke duk hayaniyar zabe ta lafa don za su dauki mataki a kan duk wanda ya yi wa jam’iyyar abin da bai dace ba.
Sanata Abdullahi Adamu, ya ce to amma duk da rashin nasara a Kano, suna gode wa Allah da Ya ba su nasara a zaben shugaban kasa da kuma a wasu jihohin.
Ya ce, “ Zaben ma da ake jira za a kammala a Adamawa da Kebbi, mu ne za mu ci in Allah Ya yarda har ma mu je mu yi guda.”