Katsina Ta Yi Na Hudun Karshe A Jadawalin Cin Jarabawar Kammala Sakandire A Najeriya
Wata Ƙungiya Ta Bayyana Kaɗuwar ta kan rashin Ƙoƙarin Ɗaliban Katsina a Jarabawa WAEC
Ƙungiyar Fitattun Mata ta Ƙasa reshen Jahar Katsina wato- High-Level Women Advocates (HILWA) a ranar Lahadin da ta gabata ta bayyana damuwarta kan yadda Ɗaliban jihar Katsina basu yi ƙoƙari ba a jarrabawar kammala sakandare ta Ƙasashen Yammacin Afirka ta 2022 (WASSCE).
Jami’ar Ƙungiyar, Dakta Binta Ado, ta bayyana damuwar ta ne, a wajen rufe taron kwanaki biyu da Ƴan Majalisar dokokin jihar Katsina da sauran masu ruwa da tsaki suka gudanar a Kano.
Mahalarta taron sun tattauna kan Ƙudirin da HILWA ta tsara domin neman a samar da kaso 35 cikin 100 na mata a fannin ilimi.
Har ila yau, sun tattauna batun aiwatar da dokar tilasta wa dukkan yara damar samun ilimi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa sakamakon WASSCE na 2022 ya nuna cewa Ɗaliban Najeriya sun yi kashi 5 cikin dari fiye da abin da suka yi a shekarar 2021 a fadin kasar.
Binta Ado ta ce, rahoton ya nuna cewa jihar Katsina ta zo ta 33 a cikin jihohi 36 na Tarayya da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ta kuma danganta rashin samun nasarar musamman a tsakanin ƴaƴa mata a jihar Katsina da karancin Shugabannin Makarantu Mata da Malamai da manyan Malamai a Makarantu.
“Muna jin cewa idan aka samu ƙarin Malamai mata, manyan malamai, da shugabannin Makarantu Mata, ƙoƙari ƴaƴa mata zai ƙaru.
“A halin yanzu, Malaman makarantun Nazare a Jihar su 987, daga cikinsu
508 maza ne, yayin da 479 mata ne; wanda ke ba mace kashi 49 cikin dari.
“Makarantun Firamare na Gwamnati muna da malamai 24,194, daga cikinsu 18,060 Maza ne, yayin da 6,134 kacal mata ne, inda aka baiwa mata kashi 25 kacal.
“A Kananan Makarantun Sakandare (JSS), muna da Malamai 4,943 daga cikinsu 3,954 maza ne, yayin da 989 ne kawai Malamai Mata, wanda ya baiwa mata kashi 20 kacal.
“A Manyan Makarantun Sakandare (SSS) muna da malamai 4,872, 4,031 daga cikinsu maza ne, yayin da 841 mata ne, wanda Mata nada kashi 17 cikin 100. Wannan ita ce kidayar da aka gudanar a duk shekara a jihar Katsina,” inji ta.
A cewarta, Jimillar mata a makarantun firamare da sakandare kashi 28 cikin 100. Haka abin yake faruwa a dukkanin ɓangarorin ilimi a jihar Katsina.
Ado ta yi nuni da cewa, jihar Katsina na daya daga cikin jahohi biyar da suka koma baya ta fuskar rajistar shiga Makaranta, da kuma kammala karatunsu, musamman a tsakanin yara mata.
“A mafi yawan lokuta, iyaye ba sa barin ‘ya’yansu mata su ci gaba da karatunsu a makarantu, duk da muna da ƙarancin Malamai Mata,” in ji ta.
Da yake mayar da martani, Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Alhaji Shehu Dalhatu-Tafoki ya yi alkawarin cewa Majalisar za ta zartar da kudirin kafin karshen wa’adin ta.
UNICEF, HILWA, da Gwamnatin tarayya da na Jihohi ne suka shirya taron, kuma ofishin kula da harkokin kasashen ketare da ci gaba na kasar Birtaniya ne suka ɗauki nauyin taron.