
Daga Sulaiman Ciroma
@katsina city news
Jirgin yakin neman zaben Dan takarar gwamnan jihar Katsina Sanata Yakubu Lado Danmarke a karkashin jam’iyyar PDP ya dira karamar hukumar Dutsi yayin da ya samu kyakkyawar tarban magoya bayan Jam’iyyar daga sassa daban-daban.
Tun a kwanakin baya dai dan takarar gwamnan tare da abokanan takararsa na jam’iyyar suka bazama lungu da sako na ko wace karamar hukuma dake fadin jihar don yada manufar takararsu ga al’ummar jihar Katsina.
haka kuma kamar yadda aka saba al’ummar karamar hukumar Dutsi sun karbi bakuncin dan takarar gwamnan tare da mukarrabanshi a harabar ofishin jam’iyyar PDP dake karamar hukumar Dutsi. kazalika kuma taron ya samu halartar dimbin jama’a daga ko wane sashe yayin da suka bayyana mubaya’ar su ga dan takarar gwamnan jihar Katsina karkashin inuwar PDP da sauran ‘yan takarkarun jam’iyyar.
A tare da dan takarar gwamnan Sanata Danmarke, akwai dan takarar Sanata na shiyyar Daura Ahmad Babba Kaita, sannan tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina mai ci Wanda ya sauya sheka daga APC zuwa PDP Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa da sauran mukarraban sa ‘yan takara wanda ya samu rakiyarsu kafada da kafada zuwa filin taron.