Sanata Umar Ibrahim Tsauri babban Sakataren jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, yace;! “lallai kamar yanda Gwamnatin Najeriya tace wai tana kashe tsabar kudi har naira biliyan goma sha takwas 18 a kullum don tallafin mai, to ba zamuce Gwamnati tayi karya ba, saidai muce ta fitar da zancen ba daidai ba.”
Sanata Tsauri yace Maganar sam batayi kama da hankali ba, yace to amma ai ‘yan Najeriya su da kansu zasuyi ma kansu hukunci, idan gaskiya ne suna ji inkuma akasin haka ne sunsani. Tsauri yace Gwamnati APC ruwane ya karewa Kada shiyasa babu komai a cikinta sai kame-kame. A karshe tsauri yayi fatan shekara mai zuwa lokacin kada kuri’a ga ‘yan Najeriya.
Source:
Katsina City News
Via:
Zaharadeen Mziag