Gwamna Aminu Bello Masari ya yaba ma Alhaji Dahiru Bara’u Mangal a kan yadda yake sa kishi da taimakon al’umma a cikin al’amurran shi.

Gwamnan yayi wannan yabon ne a yau bayan da ya kammala ziyarar da ya kai kamfanin shinkafa na Darma (Darma Rice Mills) wanda hamshakin Dan kasuwar yake ginawa a nan Katsina, wanda ya zuwa yanzu an kammala kashi na farko har shinkafa ta fara shiga buhu.
Wannan kamfani da Gwamna Masari ya aza harsashin gina shi a ranar Lahadi 16 ga watan Yuni na shekarar 2019, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal ya kudurci kafa shi ne domin amsa kiran Shugaban kasa Muhammadu Buhari na mu koma gona kuma mu inganta noman ta yadda za mu rika ciyar da kanmu.
Da farko an yi niyyar kammala kashin farko na aikin, wanda zai iya samar da tan 300,000 na shinkafa a shekara, a cikin watanni 18, amma saboda gittawar matsalar Korona, sai aikin ya sami tsaiko, amma Alhamdu lillah ya zuwa yau kusan wannan aiki na kashin farko yazo karshe, sai dan abinda ba a rasa ba.
Wani abin burgewa a wannan kamfani baya ga samar da ayyukan yi ga dubban mutane, kamfanin shi ne irin shi na farko a nan kasar, wanda ake iya dorawa a bisa wani saitin na’ura mai kwakwalwa da zai iya aiki da kan shi, misali cikin dare, iyaka da gari ya waye sai dai a kwashi tsabar shinkafa. Haka kuma yana sama ma kanshi wutar lantarki daga tururin zafin da yake fitarwa wajen turara shinkafar, wanda hakan shi ma wannan kamfani shi ne na daya a duk fadin kasar nan.
Gwamnan, wanda farin cikin shi ya bayyana a fili, ganin yadda wannan kamfani ya kama aiki, yayi kira ga wadanda alhakin tafiyar da kamfanin yake hannun su dasu sadaukar da kawunan su wajen ganin cigaba, habaka da kuma dorewar kamfanin.
Wannan shi ne burin wanda ya kafa kamfanin, hakan kuma ne zai tabbatar da dorewar karuwar duk wadanda wannan kamfani ya shafa, tun daga masu noma shinkafar, ma’aikatan kamfanin har ya zuwa ‘yan kasuwa da za su rika sayar da ita a kasuwanni.
A nashi jawabin, Alhaji Dahiru Mangal ya mika godiyar shi ga Allah da ya bashi ikon ganin wannan kamfani ya fara aiki, ya kuma gode na gwamnatin jiha a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari bisa ga dumbin goyon bayan da ya samu, tun daga fara maganar wannan aiki har ya zuwa yanzu.
Ya kuma bada tabbacin nan ba da jimawa ba, wannan shinkafa mai suna ‘MANGAL RICE’ za ta cika kasuwannin mu na gida har ma da na kasashen wajen.