Yau Litinin a ƙaramar hukumar Ɓatagarawa ta jihar Katsina, Inda magoya bayan Jam’iyyar APC a ƙarƙashin ƙungiyar “Asiwaju Gwagware gida-gida Initiative” ta Alh. Kabir Ibrahim Masari bisa jagorancin Hon. Aliyu Ilu Barde sun bayyana a Filin taro don nuna goyon bayansu ga Dikko Umar Raɗɗa da sauran ‘Yan takara na jam’iyyar APC.
Matasan da suka yi shgar bai daya a filin taron suna ta daga fastocin ‘Yan takarar shugabancin Najeriya Asiwaju da Gwagware.
Alh. Aliyu Ilu Barde ya bayya cewa kungiyar Asiwaju Gwagware gida-gida Initiative ba kamar sauran kungiyoyi ba, saboda ita tafi karkata da tallafawa marasa lafiya da masu karamin karfi da Marayu, don neman Addu’a ga ‘Yan takara don samun Nasara.
Ayyukan da ta gudanar a baya-bayannan a bisa jagorancin sa shine kaiwa wani mai Lalurar cutar Kansar jini Tallafin naira dubu dari biyu domin sayen magani da kuma tallafawa wata mata da mijinta ya mutu ya barmata ‘ya’ya mata marayu da Naira dubu hamsin don siyan Litattafan Makaranta ga yaran.
A gefe guda kuma kungiyar ta samar da Kayayyakin Amfani irinsu Butoci, Barguna da Tabarmi fiye da dubu biyar don rabawa a makarantun tsangayu da Masallatai na jihar Katsina kananan hukumomi 34.