• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Saturday, January 28, 2023
  • Login
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Sashen Hausa

Kaddamar da yaƙin neman zaben APC a Faskari; Ƙalu-balen da muka fuskanta 

December 8, 2022
in Sashen Hausa
0
Kaddamar da yaƙin neman zaben APC a Faskari; Ƙalu-balen da muka fuskanta 
0
SHARES
30
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Zaharaddeen Mziag @Katsina City News

…Jami’an tsaron DSS sun ragargazama Abokina Kyamara,

…..Mimbarin Siyasa ya rufta

Ƙaramar hukumar Faskari mai nisan Kilomita 170 daga garin Katsina,  tana ɗaya daga cikin ƙananan hukumomi 8 mafiya hatsari na ‘Yan bindiga a jihar Katsina (Koda yake zamu iya cewa Lamarin ya ɗan yi sauƙia) amma da ganin yanda Dajin na Faskari yake kasan ba’a rasa miyagu.

A dai-dai wannan lokaci na buga gangar Siyasa ne ‘Yan takarkaru daban-daban suke shiga lunguna inda suka san Dan adam yana rayuwa don neman kuru’un jama’a.

Jam’iyyar APC mai mulki ta zaɓi ƙaramar hukumar Faskari domin ƙaddamar da fara yaƙin neman zaben shekarar 2023 (mai yiyuwa don Ansamu saukin raguwa ɓarayin ‘yan bindigar). Ina ɗaya daga cikin ‘Yanjarida da Ofishina ya tura domin sheda taron kaddamar da fara yaƙin neman zaɓen.

Tun da Yammacin Ranar Lahadi Mai gidana, Malam Danjuma Katsina ya sanar da ni cewa, zanje Faskari da ni da abokin Aikina.

Mai gida Malam Danjuma ya tambaye ni, ta yaya zamu shirya Tafiyar? Ban cika son bin Motar ‘Yan Siyasa ba saboda wasunsu suna gudu na wuce Doka, suna ganganci. Sai na zaɓi muje Tashar Mota mu hau ta haya, kafin nan mai gidana ya bani zaɓi cewa ko zamu samu Shatar mota ne, ta kaimu kai tsaye? Don samawa kanmu sauƙin tsada, nace zamu hau ta haya ɗin. 

 Bisa al’ada idan zanje wani garin taro kuma a motar haya, nakan fita tun da wuri, saboda kaucewa Matsalolin tsaiko busa hanya. Karfe shida na safe na fito muka hadu da abokin tafiya. Mun yi sa’a a tashar Nato muka samu Motar zuwa garin Kankara ko wannen mu ya biya ₦1200 ba tare da jira ba Motar ta tashi, saboda mun samu wasu fasinjoji a ciki. ‘Nasara ta farko’

Mun isa garin Kankara a kan lokaci saboda 8 da rabi batayi ba muna cikin garin Ƙanƙara. Anan muka fito muka nemi dan ruwan zafi muka jika hanjin mu. Daga nan muka koma tasha muka nemi Motar zuwa Faskari Babu ‘Mafarin Matsala’.

Kada a manta zamuje taro ne, taronnan kuma ba mu za’a jira ba. Kunsan Danjarida idn yaje neman labari bai samu ba, ji yake kamar an kasashi a neman Aure.

Bayan mun fahimci cewa lallai ba za’a samu Motar Faskari ba, sai muka yanke shawarar hawa motar da ta samu, zuwa inda ya samu, “Motsi yafi laɓewa” a nan muka hau Motar Sheme, muka bi Titin da su kansu Drebobin tsoron Hanyar suke, sunce mana itace hanya mafi hatsari, wato daga Kankara zuwa Sheme har zuwa Faskari hanyar fargaba ce.

Ba zanyi batun yanda Titinan wajen suka ragargaje babu gyara ba, sai dai inyi fatan Allah yasa ‘Yan takarar mu subi hanyoyin kuma idan sunbi su shiga ramukan don suji su gyara idan an samu madafun iko.

Munyi tafiya mai dan Nisa daga karshe muka zo garin Sheme,  wajen karfe 11, shi kuma taron ance goma za’a farashi.

Muna isa Direba ya juye mu, babu Mota, nan ma mun kusa awa guda, ba mota ba alamar mota. Muna nan muna jiran tsammani gami da buge-bugen waya don nemawa kai mafita.

Sai ga wata Mota Shaƙe da Mutane (a gaskiya babu inda za’a sanya ko mutum daya bisa dadin rai a motar) Motar kamar kirar Sharon ce, dayake tashe Fosta ba kasafai zamu iya ganin sunanta ba. Motar ta Ɗan Unguwar mu ce, Direban Motar Ɗan’uwa na ne, cikin motar kusan duk ‘yan unguwa da kanne ne, za-su wajen taron na ɗaga hannu, ‘Yan’uwantaka tai rana’ ya tsaya.

Duk wannan Labarin da nake bayarwa ban sanar da mai Karatu mu nawa bane muka taho tun daga gida. To mu hudu ne 4. Muhammad Kabir “Taskar Labarai” Auwal Isa “Katsina Gazette” Aminu Salisu “Katsina Breaking News”, sai Zaharaddeen Ishaq Abubakar “Katsina City News” a haka bawon Allah nan yace bai yadda ya barmu nan ba, da yake tsohon hannu ne ya iya haggu ya iya dama, saida ya lodemu a cikin motar nan, bansan inda ya jefa mutum biyu ba a gaban motar nan, amma mudai da ni da Katsina Breaking News, mun tsinci kanmu cikin But din motar kamar jikkuna.

Zanci gaba 

www.katsinacitynews.com

Hoto 📸 Zaharaddeen Mziag

Share

Related

Source: Katsina City News
Via: Katsina City News
Previous Post

FARASHIN KAYAN AMFANIN GONA A KASUWAR BATSARI TA JIHAR KATSINA.

Next Post

Dan Guruf ya samu Babban Muƙami a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa

Next Post
Dan Guruf ya samu Babban Muƙami a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa

Dan Guruf ya samu Babban Muƙami a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa

Recent Posts

  • Buhari inaugurates 12 projects in Katsina
  • ZA AYI TAGWAYEN HANYOYI DAGA KOFAR SORO ZUWA KOFAR GUGA
  • PRESS STATEMENT: Old Naira Notes:Kano Govt,Islamic Clerics Calls On Federal Govt To Extend Naira Redesign Deadline
  • Sanarwa! Sanarwa!! Sanarwa!!! Hukumar Sufuri ta KTSTA zataci gaba da amsar tsaffin kudi
  • Dala Inland Dry Port: Kanawa Ga Na Ku
    By Adamu S. Ladan

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In