• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Friday, March 31, 2023
  • Login
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Sashen Hausa

Ka Gaji Da Shan Maganin Ciwon Gwiwa Kullum!

October 3, 2022
in Sashen Hausa
0
Ka Gaji Da Shan Maganin Ciwon Gwiwa Kullum!
0
SHARES
49
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga Shafin Physiotherapy Hausa

Daga cikin nau’o’in ciwon gwiwa da mutane ke fama da shi akwai ciwon gwiwa wanda ake cewa “amosanin gaɓar gwiwa”, wato “Knee Osteoarthritis” a turance, wannan ciwo ne da har a yanzu wasu mutane ke da tunanin ciwon sanyi ne. Tabbas wannan ciwo ba shi da alaƙa da sanyi ko kaɗan.

Irin wannan ciwon gwiwa yana faruwa ne sakamakon zaizayewar gurunguntsin gaɓa wanda shi ne matashin da ke tsakanin ƙashi da ƙashi domin ƙasusuwan gwiwar su riƙa gogayya da juna ba tare da tirjiya ba.

Kasancewar gaɓar gwiwa gaɓa ce da ke ɗawainiyar dakon nauyin jiki tun daga kai har zuwa gwiwa a lokutan tsaiwa ko tafiya da kuma buƙatar motsawarta a mafi yawan lokuta yayin zirga-zirga. Haka ne ya sa ciwon ke kama gwiwowin biyu duka duk da cewa ciwon gwiwa ɗaya na iya fin na ɗayar a lokaci guda.

Bincike ya nuna cewa wannan ciwon gwiwa na gaba-gaba a jerin larurorin da ke iya nakasa mutum sannan kuma ya tsugunar da mutum ɗungurugum! Saboda haka, tasirin ciwon yana da babbar illa ga ingancin rayuwa, walwala da tattalin arziƙin masu fama da shi.

Alamun ciwon amosanin gwiwa

Masu irin wannan ciwon gwiwa suna fama da:

1) Ciwo mai ɗabi’ar tsuko a cikin gwiwa, musamman da daddare ko da safe kafin fara tafiya.

2) Kumburin gwiwa.

3) Riƙewar gwiwa.

4) Idan ma ciwon ya ta’azzara a kan ji sautin gugar ƙasusuwan — ƙurus-ƙurus yayin lanƙwasa ko miƙar da gwiwar ko kuma yayin tafiya.

Haka nan, yau da gobe ciwon gwiwar kan haifar da sauye-sauye a gaɓar gwiwa tun daga ƙasusuwa, zuwa gurunguntsi, tantanai da kuma tsokokin da ke aiki a kan gwiwar. Misali, raguwar tazarar da ke tsakanin ƙasusuwan gwiwa (saboda zaizayewar gurunguntsin gaɓa), ɗaurewar tsokokin cinya na baya da kuma raunin tsokokin cinya na gaba, da dai sauransu.

Masu haɗarin kamuwa da ciwon amosanin gwiwa sun haɗa da:

  1. waɗanda shekarunsu suka miƙa.
  2. masu ƙiba.
  3. masu haɗarin samun rauni ko bugu a gwiwa, musamman ga masu wasannin guje-guje da tsalle-tsalle.

4) waɗanda sana’o’insu ke buƙatar ɗaukan nauyi tare da daɗewa a tsaye.

5) masu wasu nau’o’in tawayar gwiwa kamar cassa / gwame da sauransu.

Kasancewar wannan ciwo yana farawa ne kaɗan da kaɗan, kuma yana da matakan ciwo da nakasu hawa-hawa.

Matakan ciwo ko nakasun gwiwa:

Akwai matakin farko, mataki na biyu da mataki na uku.

1) Mataki na farko shi ne yake da mafi ƙarancin ciwo da nakasu.

2) Mataki na biyu kuwa shi ne matsakaicin ciwo da nakasu.

3) Sai mataki na uku shi ne lokacin da zaizayewar ta kai matuƙa kuma shi ne mafi tsananin ciwo da nakasu.

Domin haka, samun sauƙin wannan ciwon gwiwa yana da alaƙa da ɗaukar matakan gaggawa tun da wuri domin fara shawo kan ciwon. Misali, matakin farko na ciwon zai fi sauƙin magani a kan mataki na uku. Saboda haka, akwai matuƙar buƙatar garzayawa asibiti da zarar an fara jin ciwon gwiwa domin shawo kan ciwon cikin gaggawa.

Sai dai, yawancin masu fama da wannan ciwo na ɗaukar ɗabi’ar nan ta shan magungunan rage ciwo barkatai domin rage raɗaɗin ciwon gwiwar. Amma waɗannan magunguna ko kaɗan ba sa warkar da wannan ciwo, sai dai su kan iya rage raɗaɗin ciwon na wani ɗan lokaci kawai. Saboda waɗannan magunguna suna da ƙayyadajjen lokaci da suke ɗauka suna aiki a jikin mutum, idan lokacin aikinsu na rage ciwo ya ƙare, to ciwo zai dawo har sai an sake shan wani maganin kuma.

To yaushe mutum zai daina shan maganin kenan?

Tabbas babu lokacin daina shan maganin rage ciwo idan ba a je wurin ƙwararrun likitocin da ya kamata ba.

Likitocin fisiyo (Physiotherapists) ne ke lura da masu irin wannan ciwo. Waɗannan likitoci suna dubawa, sannan su rage ciwon a sauƙaƙe ta hanyar amfani da na’urorin rage ciwo na zamani ba tare da shan magunguna ko dogaro da magani kullum ba.

Bayan nan, za su bayar da keɓaɓɓun atisaye na musamman na ciwon gwiwa domin tsokokin da ke aiki a kan gwiwa su sami ƙarfin iya riƙe ƙasusuwan gwiwar yadda ya kamata ba tare da suna gugar juna ba.

Sannan suna koyar da dabarun motsa jiki a cikin ayyukan yau da kuluum domin kiyaye ire-iren motsin da ka iya ta’azzara ciwon.

Daga ƙarshe, idan duk waɗannan hanyoyi ba su yi nasarar shawo kan wannan ciwo ba, hakan na iya tilasta ɗaukar matakin ƙarshe wajen magance ciwon, wato ɗaukan matakin yin tiyata/aiki domin yin dashen gwiwa da zai maye gurbin zaizayayyen gurunguntsin gaɓar. Ana ɗaukar matakin yin tiyata/aiki ne idan ba a fara ganin likitan fisiyo da wuri ba har sai da ciwon ya nakasa gaɓar gwiwar.

Idan kana fama da ciwon gwiwa kuma ka gaji da shan magani kullum, tuntuɓi likitan fisiyo (Physiotherapist) a yau domin fara bankwana da ciwon gwiwa.

Share

Related

Source: Katsina City News
Via: [email protected]
Previous Post

“Tun Ina jami’a nake Aikin Zabe Amma bantaba Amsar Kudin Kowaba”

Next Post

“Akwai wani labari da na jima da sani, wanda duk wanda ya yi aiki da Kwankwaso a kusa-kusa ya sani.” -Jaafar Jaafar

Next Post
“Akwai wani labari da na jima da sani, wanda duk wanda ya yi aiki da Kwankwaso a kusa-kusa ya sani.” -Jaafar Jaafar

"Akwai wani labari da na jima da sani, wanda duk wanda ya yi aiki da Kwankwaso a kusa-kusa ya sani." -Jaafar Jaafar

Recent Posts

  • On birthday, clerics pray for Tinubu, Nigeria in Abuja
  • Gwamna Masari ya Kaddamar da Kwamitin Miƙa Mulki ga sabuwar Gwamnati
  • Masari: Tinubu Na Bukatar Addu’a
  • Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Karu Zuwa N46.25tr —DMO
  • FEC Approves N59.78bn For Ogoni Cleanup Projects

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • March 2023
  • February 2023
  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In