An kwashi ƴan kallo bayan da a jiya Alhamis wani jirgin kasa mai tafiya ya tsaya wa wani mutum da ke zaune a kan titin jirgin da ke kan hanyar Cappa/Oshodi.
Mutumin, kamar yadda binciken Daily Trust ya nuna, yana zaune ne a kan layin dogo bayan da aka ce ya zubar da kuɗinsa har Naira dubu 35, inda ya ci gaba da zama a wajen duk da ƙarfin ƙarar ham ɗin jirgin da ke tunkaro wa wajensa.
Abin da ya ba wa mutane da yawa mamaki, kawai sai a ka ga jirgin kasan na Legas zuwa Ibadan ya tsaya jira mutumin ya tashi, sannan ya ci gaba da tafiya.
Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya zauna a kan titin ya ki tashi duk da ƙarfin ham ɗin jirgin, mutumin ya bayyana cewa ya zubar da kuɗinsa ne Naira dubu 35 a kan hanyarsa ta zuwa kasuwa.
Wata majiya ta jirgin kasa da ta zanta da Daily Trust ta ce mutumin ya yi sa’a saboda yawaitar mutane da ke kewayen yankin, domin a kodayaushe jirgin yana rage gudu idan ya tunkaro yankin.
Hakan na zuwa ne ‘yan makonni bayan da jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya murkushe wata mata da ke tuki a kan titin jirgin har lahira.