Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar hallaka wasu manyan ƴan ta’addan ISWAP biyu, Ali Kwaya da Bukar Mainoka.
An kashe su ne a wani samame da jiragen yakin sojin Najeriya suka kai a tafkin Chadi a jiya Asabar, kamar yadda PRNigeria ta tattaro.
Kwaya da Mainoka, wadanda su ma manyan mambobin shura ne na ISWAP sun gamu da ajalinsu lokacin da Rundunar Sojan Sama ta Operation Hadin Kai ta kai farmakin sama a Belowa, daya daga cikin tsirarun maɓoyar ISWAP da Boko Haram da su ka rage a Tumbuns. , yankin tafkin Chadi a karamar hukumar Abadam.
PRNigeria ta tattaro daga wani jami’in leken asiri na soji cewa harin da suka kai ta sama a Belowa ya zama dole bayan bayanan sirri sun bayyana haduwar wasu shugabannin ISWAP da mayakan da ke kewaye domin ganawa da manufar shirya kai hare-hare.
A cewar jami’in, wanda ya nemi a sakaya sunansa, an aika jiragen yakinsu na rundunar sojin sama zuwa wurin taron ƴan ta’addan a Belowa, inda s ka artabu da ‘yan ta’addan na ISWAP da rokoki da bama-bamai.
“Sa’a daya bayan harin, a ka hallaka motoci 2 dauke da ‘yan ta’adda kusan 13 da suka samu raunuka zuwa wata maboyar ta jirgin na NAF.
“Sakamakon harin ya nuna cewa wani kwamandan ISWAP, Malam Ali Kwaya wanda babban mamba ne a Majalisar Shura ta ISWAP da Malam Bukar Mainoka na daga cikin wadanda aka kashe a harin,” in ji shi.