©️BBC Hausa
Yayin da ake shirin kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha a Najeriya a ranar Asabar mai zuwa, akwai wasu jihohi na daban guda shida da ba za a yi zaɓen gwamna a cikinsu ba.
Jihohin su ne:
Anambra
Bayelsa
Edo
Ekiti
Kogi
Ondo
Osun.
Wannan ya biyo bayan hukuncin kotu na rushe wasu zaɓuka da aka yi a baya tare da tabbatar da wasu da aka zaɓa waɗanda da farko ba su aka bayyana ba a matsayin masu nasara.
Sai dai a duka jihohin za a gudanar da zaɓen ‘yan majalisun jiha kamar yadda aka tsara tun da fari.
Wannan rashin daidaiton zaɓe tsakanin jihohin shida da sauran jihohin ƙasar ya zamar wa hukumar zaɓe ta INEC wani abu na koma baya, ganin kowacce jiha sai dai a yi mata nata shirin daban.
Hakan dai ya samo asali ne tun a 2003 lokacin da aka gudanar da zaɓen jihar Anambra a watan Afrilu.
Aka bayyana Dr. Chris Ngige na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓe, aka kuma rantsar da shi a matsayin gwamna ranar 29 ga watan Mayu na 2023, tare da duk wanda aka zaɓa.
A wannan lokaci Peter Obi ne ke takarar gwamnan jihar a jam’iyyar APGA, ya nuna bai gamsu da wannan sakamako ba, abin da ya kai shi ga shigar da ƙara gaban kotu kenan.
Bayan shekara uku ya samu nasara kan shari’ar da ya shigar gaban kotun sauraren ƙararrakin zaɓe, a ƙarshe dai a watan Maris na 2006 a ka rantsar da shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar.
Ko da aka zo gudanar da zaɓe a 2007, Obi bai shiga zaɓen ba, hakan ya sanya aka bayyana Andy Uba a matsayin wanda ya lashe zaɓen ƙarakashin jam’iyyar PDP.
Daga baya kotu ta ƙara yanke hukuncin cewa Obi ne gwamna domin wa’adin mulkinsa bai ƙare ba, ta kuma yi bayani kan cewa “ wa’adin gwamna na farawa ne kawai daga ranar da aka rantsar da shi,” in ji kotu.
Tun daga wannan lokaci ne aka samu sabani wajen gudanar da zaɓe a jihar ta Anambra.
Irin wannan lamari ne ya faru a jihar Edo a ranar 14 ga watan Afrilun 2007, lokacin da kotun saurarren kararrkin zaɓe ta ayyana Adams Oshiomhole a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar kuma ‘yan taccen gwamna.
A 2010 ma, haka aka yi lokacin da kotu ta ayyana Kayode Fayemi a matsayin gwamnan Ekiti, ba a sake zaɓe a jihar ba sai 2014, maimakon 2011.
A watan Agustan 2008, kota a jihar Ondo ta ayyana Dr. Olusegun Mimiko na jam’iyyar LP a matsayin gwamnan da ya lashe zaɓen jihar.
Kotun ta kwace mulki ne daga hannun Olusegun Agagu na jam’iyyar PDP wanda aka rantsar tare da sauran waɗanda suka ci mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2007.
Irin waɗannan tarin matsaloli da shari’u ne suka taru suka haifar da jinkiri a wajen daidaita zaɓe tsakanin waɗannan jihoji da sauran da za a gudanar da zaɓensu a ranar Asabar 18 ga watan Maris.