Zaharaddeen Mziag @Katsinq City News 11/11/2022
Taron baje kolin ra’ya al’adun da yake gudana a Birnin Lagos wanda Gwamnan jihar Baba Jide Sawo Olu ne ya kaddamar da shirin karo na talatin da biyar 35 a filin wasa na ƙasa dake Birnin Lagos. Shirin na Bana wanda aka fara tun daga ranar bakwai 7 ga watan nan har ya zuwa ranar sha uku 13 ga watan Nuwamba zai samu halartar jihohi 25 da Babban Birnin Tarayya Abuja. Baba Jide ya bayyana shirin mai taken Al’adu da kuma zaman lafiya, yace shirin nada manufar bunkasa zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin ƙabilu, a lokacin da shugaban hukumar Tarihi da Al’adu na jihar Katsina Alhaji Ibrahim Danbaba ke jawabi. Ya bayyana cewar jihar Katsina na daga cikin jihohin da za’a taka da ita a Kowane mataki, da ya hada da matakin wasan kwaikwayo, abincin gargajiya da sauransu.