Daga Muhammad Kabir
Jaridar Taskar Labarai
An kaddamar da Bude kamfen na ƴan takarkarun Jam’iyyar NNPP a jahar katsina a ranar Alhamis 5/01/2023.
Da yake Magana a wajen Bikin Bude kamfen din Dan Takarar Kujerar Shugabancin Kasa a jam’iyyar Mai alamar kayan marmari Engr Dr Rabi’u Musa Kwankwaso, Wanda ya samu wakilcin Dan Takarar Kujerar Gwamna a Jahar Kano Engr Abba Yusuf (Abba gida-gida).
Abba yace Idan Allah ya Basu mulki, Gwamnati tayi tanadin abubuwan more rayuwa Kamar su Ilimi, kiwon Lafiya, Noma, da samar ma da Matasa ayyukan Yi.
Ya kara da cewa “A fannin Tsaro musamman a jahar katsina za’ayi Mai yuwa wajen ganin an shawo kan Matsalar in Allah ya yarda.
Sanatoci da Yan majalissu na wannan Jam’iyyar duk kaminsu can cantattune Idan al’umma Suka Basu amanar su, ba Zasu ci amanaba.
Daga Karshe Yayi fatan al’umma Zasu fito ranar zaɓe su Zaɓi Jam’iyyar NNPP, Kuma su tsare, su raka, su Jira.
A Nashi Jawabin Dan Takarar Kujerar Gwamna a Jahar Katsina Engr Nura Khalil yace Dalilin da Yasa ya zaɓi karamar hukumar Mashi dumin ya fara yakin Neman Zaɓen Sa shine.
Masana sun Nuna Cewa da Garin Mashi da daurawa Dake Cikin Jahar Jigawa da kankiya, a Nan akafi sanun hasken Rana Wanda za ayi wutar lantarki. Saboda haka a Cikin Wata goma Sha biyar zamu Samar da wutar lantarki mai manfani da hasken rana a garin Mashi Wanda Zai kama mega wad dubu (1000).
Dan takarar yace idan ya zama Gwamna matsalar tsaro zata zama Tahiri a Jihar.