Jami’ar tarayya ta garin Dutsin-ma da jami’ar Georgia dake ƙasar Amurika sun rattaba hannu bisa wata yarjejeniya domin habba ilimin koyo da koyarwa da bincike a tsakanin jami’o,in biyu. Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jami’ar Habibu Umar Aminu ya fitar yace rajejeniyar an yita ne kan shekaru biyar, kuma angudanar dashi akan yanar gizo inda mataimakin shugaban jam’iyyar Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi ya wakilci jami’ar ta Dutsinma a yayin da Dakta Dariyo ya wakilci jami’ar Georgia a yayin rattaba hannun. An cimma yarjejeniyar Bunkasa bincike kan fannin Ilimin rayuwar Al’umma wato Biology da sauran fannoni da suka shafi fannin. Sauran sune samar da mukalar Ilimi Wato Acadamic Journal da bincike domin amfanin jami,o’in biyu da kuma samar wa jam’iyyar damar karin karatu ga malamai da ma’aikata da sauransu.
Da yake jawabi jum kadan bayan kammala rattaba hannun, mataimakin shugaban jam’iyyar Farfesa Armaya’u Bichi Ya danganta sanya hannun da wani yunkuri na cigaba da zai bunkasa koyo da koyarwa a tsakanin jami’o,in biyu Farfesa Bichi ya tabbatar da kudirinsa na cigaba da lalubo Damarmaki ga malamai da daliban jami’ar Dutsinma, domin bayyana irin kwarewar da jami’ar keda shi a bangaren bincike da koyar wa.