Rundunan ‘yan sanda a jahan kano dake arewacin nijeriya ta sanar da kama matasa 93 bisa zarginsu da bangan siyasa da tayarda zaune tsaye yayin da jam’iyyu ke taron yakin neman zabe.
Kwamishinan ‘yan sandan jahan Mamman Dauda ne ya tabbatar da kamen matasan ta cikin wata sanarwa daya fitar mai dauke da sa hannun kakakin rundunan ‘yan sanda Abdullahi Haruna Kiyawa.
Kwamishinan ‘yan sandan ta cikin sanarwan yace, an kama matasan ne bisa umarnin babban sufeton ‘yan sandan kasan sufeto Usman Alkali Babba, na kakkabe dukanin matasan da ke ikirarin dabanci a kasan baki daya.
A cewanshi an kama matasan ne a wani samame da ‘yan sandan suka kai filin taro na Sani Abacha dake jahan lokacin da wata jam’iyya ke taron yakin neman zaben ta.
A cewanshi an kama matasan ne da bindigogi kiran gargajiya guda biyu, da wukake guda 32, da adda guda 1, sai kuma layoyi da guru masu tarin yawa.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.